Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Louis Van Gaal Ya Zama Kocin Netherlands A Karo Na Uku

  Hoto: GettyImages An sanar da tshohon kocin Manchester United, Louis van Gaal, a matsayin sabon kocin Netherlands a karo na uku. Ɗan ƙasar...

 

Hoto: GettyImages

An sanar da tshohon kocin Manchester United, Louis van Gaal, a matsayin sabon kocin Netherlands a karo na uku.

Ɗan ƙasar ta Netherlands mai shekara 69, Van Gaal ya maye gurbin Frank de Boer, wanda ya ajiye aikinsa a watan da ya gabata biyo bayan cire ƙasar da aka yi a zagayen 'yan 16 da Czech Republic ta yi a gasar Euro 2020.

Van Gaal ya ja ragamar tawagar daga 2000 zuwa 2002 sai kuma a 2012 zuwa 2014, inda daga bisani ya koma Manchester United.

Bai sake horar da wata ƙungiya ba tun bayan da United ta kore shi a 2016, sai dai ya ce komawarsa tawagar ta Netherlands "girmamawa" ce.

"Na daɗe ina sha'awar ƙwallon Netherlands kuma horar da ita wani mataki ne na ciyar da ƙwallonmu gaba," a cewar Van Gaal.


No comments