Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da mahukumtan jami’ar, sun t...
Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American
University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da mahukumtan jami’ar, sun
taya Hajiya Mairo Saidu murnar nadinta a matsayin Shugabar Makarantar Aikin
Jinya da Unguwanzoma ta Kano wato ‘School of Nursing and Midwifery’.
Hajiya Mairo Saidu ta kammala karatun ta a Jami'ar Maryam Abacha
American University dake Jamhuriyyar kasar Nijer.
Sakon taya murnar na dauke ne a takardar da Farfesa Abubakar Gwarzo
ya sanyawa hannu kuma aka rabawa ‘yan jarida a Kano a ranar Laraba.
Shugaban MAAUN ya bayyana nadin Hajia Mairu Saidu a matsayin
shugabar makarantar da gwamnatin jihar Kano ta yi a matsayin; “nadin da ya
cancanta' idan aka yi la'akari da gogewa da aiki tukuru yayin da take daliba a Jami'ar”.
Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana fatansa na cewa nadin da aka yi
mata za ta yi amfani da godewarta wajen gudanar da Kwalejin da zimmar ciyar da
makarantar gaba.
“a madadin kaina da iyalina
da hukumar gudanar da MAAUN, ina son taya ki murna bisa nadin da aka yi miki a
matsayin shugabar Kwalejin Aikin Jinya da kuma Unguwanzoma ta Kano”, inji
Farfesa Gwarzo.
Ya kara da cewa; “Da fatan Allah madaukakin Sarki ya taimake ki
wajen sauke sabon nauyin da aka dora miki”, inji Farfesa Gwarzo a takardar da
ya rubuta.
A karshe ya yi addu’ar Allah madaukakin Sarki ya bai wa Hajia Mairo
Saidu kwarin guiwa, jajircewa da hikimar shugabantar Kwalejin cikin adalci da
daidaito.
No comments