Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Masarautun Gargajiya Cibiyoyin Haɗin Kan Al'umma Ne- Gwamnan Neja

Na biyu daga dama; Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello Sai Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero a yayin bukin mika masa sandar girma a matsay...

Na biyu daga dama; Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello
Sai Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero a yayin bukin mika
masa sandar girma a matsayin Sarki mai daraja ta daya


Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya ce masarautun gargajiya wuraren haɗin kan al'umma ne a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da Sakatariyar watsa labaran gwamnan Mary Noel-Barje ta fitar, ta ce Gwamna Sani Bello ya bayyana hakan ne yayin bikin naɗin sarauta da gabatar da sandar mulki ga Sarkin Bichi na biyu, Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar a masarautar Bichi.

Ya ce haɗuwar Sarakunan gargajiya daban-daban a jihar don shaida naɗin sarautar Sarkin Bichi, yana ƙara tabbatar da cewa haɗuwarsu za ta haifar da haɗin kai tsakanin ƴan Najeriya kamar yadda za su yi koyi da juna.

Gwamnan ya ce naɗin Sarkin Bichi zai kawo ci gaban gaggawa a masarautar tare da samar da zaman lafiya da tsaro.

Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari wanda ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya, ya bayyana Sarkin a matsayin masani wanda zai yi amfani da gogewarsa don samar da ci gaban da ake buƙata a masarautar sannan ya tabbatar wa Masarautar ci gaba da tallafawa gwamnati a yankin.

Da yake gabatar da sandar mulkin, Gwamna Ganduje ya buƙaci Sarkin da ya ci gaba da gudanar da shirye -shirye da manufofi da za su canza masarautar, jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero a cikin jawabinsa, yayi alƙawarin zai yiwa kowa adalci, yayin da ya tabbatarwa da taron cewa shugabancin sa zai fi ba da muhimmanci ga aikin gona na zamani, ilimin addinin musulunci da na boko.

Ya yi ƙira ga jama'a da su kasance masu lura da tsaro, sannan ya yi ƙira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafa musamman wajen magance kwararowar hamada a masarautar.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III yana cikin sauran masu jawabi a wajen taron, ya tabbatar wa masarautar goyon bayansa tare da rokon Allah da ya ba wa Sarki hikimar jagorantar al'ummar sa bisa daidai.

No comments