Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Matawalle Ya Dage Kan A Kafa Dokar Ta-Ɓaci A Jihohin Arewacin Nijeriya

  Gwamnan Jihar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle ya yi kira da a sanya dokar ta-baci a duka jihohin arewacin kasar dangane da matsalar tsar...

 


Gwamnan Jihar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle ya yi kira da a sanya dokar ta-baci a duka jihohin arewacin kasar dangane da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin kamar yadda BBC Hausa ta labarto.

Ya yi wannan kira ne yayin wata tattaunawa da ya yi da mataimakin shugaban 'yan sanda da ke lura da shiyya ta 10 da ke Gusau Ali Janga.

Gwamnan, wanda ya nuna damuwa matuka kan yadda ake kai hare-hare a mafi yawan jihohin yankin, ya yi amannar cewa sanya dokar ta-ɓacin za ta taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron.

Yankin arewacin Najeriya ya hadar da shiyoyi uku, shiyyar arewa maso gaba - da arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya ga kuma babban birnin kasar na Abuja da ke yankin.

Shekaru masu yawa, yankin ke fama da ayyukan 'yan tada kayar baya da suka hada sace mutane don neman kudin fansa da tashe-tashen bam, da harin 'yan fashin daji da dai sauransu.

Kuma kafin yanzu an kashe daruruwan mutane a yankin yayin da irin wadannan rikice-rikice suka tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu domin tsira da rayuwarsu.

Kungiyar Boko Haram da ISWAP sune suka fi damun yankin arewa maso gabas, yayin da sace mutane domin kudin fansa da kuma 'yan fashin su ke damun yankin arewa maso yamma da kuma maso tsakiya.


No comments