Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mayakan Taliban Sun Kwace Iko Da Manyan Birane 3 A Rana Guda

  Mayakan kungiyar Taliban na ci gaba da mamaye karin yankuna a arewacin Afghanistan, inda a jiya Lahadi suka kame wasu manyan biranen lardu...

 


Mayakan kungiyar Taliban na ci gaba da mamaye karin yankuna a arewacin Afghanistan, inda a jiya Lahadi suka kame wasu manyan biranen larduna uku, makwanni kalilan bayan kaddamar da farmaki kan dakarun gwamnati da ke manyan garuruwa.

Kawo yanzu manyan biranen larduna 5 mayakan Taliban suka kwace a Afghanistan daga ranar Juma’a zuwa Lahadi, alamar da ke nuna zai yi wuya dakarun gwamnatin kasar su iya murkushe su ba tare da tallafi ba.

Taloqan, Kunduz da Sar-e-Pul su ne manyan biranen lardunan da Taliban ta mamaye a ranar ta Lahadi, inda wasu majiyoyi suka ce sun samu nasarar ce ba tare da yin wani kwakkwaran gurmuzu da dakarun gwamnati ba.

Kame biranen Taloqan da Kunduz ce nasara mafi girma da Taliban ta samu kan gwamnatin Afghanistan a baya bayan nan, tun kaddamar da farmaki kan sojojin kasar a watan Mayu, a daidai lokacin da dakarun kasashen waje suka fara janyewa.


No comments