Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce miƙa wuya da mayaƙan Boko Haram ke yi a jihar ya jefa ta cikin mawuyacin hali. Ya ce lamar...
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce miƙa wuya da mayaƙan Boko Haram ke yi a jihar ya jefa ta cikin mawuyacin hali.
Ya ce lamarin na buƙatar kulawar masu ruwa da tsaki da wakilan al'ummomi su hada kai wajen tabbatar da cewa an samo mafita.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai garuruwan Bama da Gwoza na jihar ta Borno.
A cewar gwamnan "mu da muke jihar Barno, muna cikin mawuyacin hali bisa miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram ke yi. Yanzu dole ne mu zaɓi cikin abu biyu masu muni: wannan yaƙin da ya ki ci ya ƙi cinyewa da kuma rungumar waɗannan ƴan ta'addar da suka miƙa wuya suke so su dawo cikinmu."
Ya ce a jihar akwai mutane da dama da ƙungiyar Boko Haram ta kashe wa ƴan uwa kuma har yanzu suna cikin alhinin mutuwarsu, don haka zai yi wuya su iya rungumar mayaƙan masu miƙa wuya har su iya rayuwa tare da su a wuri guda.
"Ko sojoji ma, wannan abu ne mai wuya a garesu saboda akwai abokan aikinsu da ƙungiyar ta kashe. Babu wanda zai iya rungumar makashin masoyinsa hannu bibbiyu," in ji Zulum.
Gwamnan ya ce amsar ƴan Boko Haram na da haɗarin bata wa ƴan uwan waɗanda aka kashe rai kuma suna ma iya yin bore, yayin da a wani ɓangaren kuma ƙin karɓarsu na iya sa mayaƙan Boko Haram ɗin su shiga ƙungiyar ISWAP su ƙara mata ƙarfi.
Gwamna Zulum ya ce zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari da manyan hafoshin tsaro da shugabannin al'umma da malaman addini da ƴan majalisar wakilai da malaman makaranta da sauran masu ruwa da tsaki musamman waɗanda lrikicin Boko Haram ya shafa don ganin an samo mafita a wannan lamari.
-BBC Hausa
No comments