MUHAMMADU SANUSI A SHEKARA 60: Nazarin Ra’ayoyinsa Da Halayyar ‘Yan ArewaDaga Ammar M. Rajab

Khalifa Muhammadu Sanusi a ranar 31 ga watan Yuli ya cika shekara 60 a duniya. Hakan ya sanya masoyansa suka taru a Kaduna domin shirya taro kan nazartar rayuwarsa da irin gudummawar da ya bayar a fannoni mabambanta, abin da suka kira ‘colloquium’ a turance.

A labarin da Jaridar Daily Nigerian ta wallafa a ranar 12 ga watan Agustan 2021, ta bayyana cewa, Sakataren kwamitin shirya taron, Isma’il Auwal, ya bayyana cewa taron zai zama na shekara-shekara ne, kuma a bana za a yi ne a dakin taro na Umaru Musa ‘Yar’adua dake Murtala Square a Kaduna.

Taron na bana an yi masa take da; ‘Muhammadu Sanusi II: Alamin kawo sauyi,’ a cewar Sakataren an shirya taron ne domin murnar nasarorin da tsohon ma'aikacin Babban Bankin ya samu a fannoni daban-daban da ya hada da zamansa masani a bangaren fasaha, Sarautar Gargajiya, da kuma addini, wanda ya ba da gagarumar gudummawa ta ban mamaki wajen kawo sauyi a arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

Muhammadu Sanusi, wanda a halin yanzu shi ne Khalifan Darikar Tijjaniyyah a Nijeriya, ya yi shura wajen bayyana ra’ayoyinsa wadanda suka sa6a wa al’adar da mutanen arewa suka dade da zama a kanta.

Daga cikin ra’ayoyin Muhammadu Sanusi akwai batun bai wa mata ‘yanci, dakile haihuwa gaba-gadi da ake yi ana watsarwa, wasu kuma a kai su ‘bara’, daina yi wa mata auren wuri, bai wa mata damar yin aiki, gina makarantu a maimaikon masallatai, da kuma ra’ayoyin da Talakawa ke ganin na jari hujja ne a matsayinsa na ‘masani’ a bangaren tattalin arziki.

Ra’ayoyin Muhammadu Sanusi na ganin talauci na da alaka da haihuwa gaba-gadi, auren mace fiye da daya, rashin kyakkyawan ilimi da kuma jahilci. Sai dai ba kasafai yake caccakar rashin kyakkyawan shugabanci ko tsarin jagorancin Nijeriya a matsayin daya daga cikin hanyoyin da ke haifar da hakan ba.

Ra’ayoyinsa da dama ya sanya talakawa da dama hannun riga da shi duba da ganin ra’ayin na sa ba ya gamsar da zuciyarsu dangane da abin da suke so. Kuma babbar barazana ce ga rayuwarsu da suke lallabawa. Sannan suna masa kallon mutumin da ba ya aikata abin da yake yawan fade. Kuma mutum ne da bai san me ake cewa wahala ba balle ya bada labarinta lura da tarihinsa da damarmakin da ya samu a rayuwa wanda mafi yawan wadanda yake caccaka ba su samu wannan damar ba.

Wadannan da ma saura na janyo masa caccaka da suka mai gauni daga ‘yan arewa. Duk da dai yana da masoya musamman daga ‘yan Boko a arewa. Wanda suke yi masa kallon ‘alamin sauyi’ da ba a girmamawa a Arewa.

Bari mu yi tuni, mu kuma taskace abin da ya faru a shekarun baya. A kokarinsa na neman goyon bayan ‘yan arewar da yake caccaka, Muhammadu Sanusi bayan kisan kiyashin da sojojin Nijeriya #ZariaMassacre suka yi a kan 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky inda aka kashe mutum fiye da dubu daya, sai tsohon Sarkin ya kada da bakinsa ya ce; 'Nijeriya kasa ce da ta doru a kan sunnah, kuma ba za su yarda a yi wani abu ba idan ba Sunnah ba', duk da Farfesa Dahiru Yahaya a nan ya jijjige wanna tarihin, inda ya kawo alkaluman Sarakunan Kano da Shi'anci suka yi. 

Idan muka yi nazarin ra'ayin Muhammadu Sanusi a nan zamu lura da cewa ra'ayi ne da ba shi da bambanci da ra'ayin kafiran Makkah da suke ganin tunda sun dade suna bautar gumakansu, ba su da bukatar wani Annabi da zai kawo musu wani sabon abin bauta. 

Kuma ra'ayin na shi a nan ba shi da bambanci da cewa: idan mutane suka dade a kiristanci har ya zama rayuwarsu na yau da kullum, to ba su da bukatar a kai musu Musulunci ya zama sabon hanyar rayuwarsu, domin kuwa sun wadatu da Kiristancinsu. 

Ra'ayinsa a nan har wala yau ba shi da bambamci da cewa; tunda 'yan Arewa sun dade suna 'tauye hakkin mata', suna kuma aurar da su da wuri, sannan suna haihuwa gaba-gadi tare da watsar da 'ya'yan wasu kuma a kai su 'bara', to ba su da bukatar 'alamin sauyin' da zai sauya wannan halayyar ta su. Eh mana! Abin da Muhammadu Sanusi ya koyar shi ne; dadewa ana aikata abu, daidai ne, kuma ba bukatar a kawo wa wannan abin sauyi. Amma kuma a lokaci guda a kashin kansa yana da ra'ayoyin kawo sauyi da yake ganin ya kamata a ce al'ummar da ya fito cikinta ta sauya. Wanda yake kan irin ra'ayin nan ne ya caccaki 'yan Shi'a musamman alamjiran Shaikh Zakzaky har yana kiran su da ''yan kauye'. 

Duk da cewa Muhammadu Sanusi ya san cewa Shi'awan da yake caccaka ba tilasta wa mutane suke yi su sauya ra'ayinsu daga 'Sunnanci' zuwa 'Shi'anci' ba, illa iyaka da'awa suke yi ba ta hantara ba, ta lumana ce da ruwan sanyi, amma haka ya runtse idonsa, ya kawar da kansa daga hakika har ya yi yunkurin tunzara 'yan Arewa su afkawa 'yan shi'a. 

Ni a kashin kaina ba ni da matsala da wasu daga cikin ra'ayoyin Khalifa Muhammadu Sanusi kan halayyar 'yan Arewa, inda nake da matsala da shi kuma tun daga lokacin na raina zurfin tunaninsa shi ne; yadda yake ganin dadewa akan abu, yana maishe da abin daidai. Tun daga wannan lokacin na fahimci cewa ta'assubanci bai bar hatta wadanda ake ganin suna da ilimi ba. 

Abu na kusa da karshe wanda nake so Khalifa Muhammadu Sanusi ya sani bayan ya cika shekara 60 a duniya shi ne; na san zuwa yanzu ya fahimci cewa wanda ya dauki hanyar kawo sauyi daga wani abu da ya ga ana aikatawa ba daidai ba a kasarnan, to tabbas sai ya fuskanci kule daga wadanda yake so ya kawo wa sauyin. Abin da Shi'awa ke fuskanta a kasarnan, yana da alaka da sauyin da suke son kawo wa ba wai don wani abu ba. Domin Shi'anci ba sabon addini bane da za a ce yau aka fara jin labarinsa. Sannan idan har yanzu Khalifa na ganin dadewar abu shi ne daidai, to 'yan arewa za su ci gaba da zama bisa al'adar da Muhammadu Sanusi ke son sauya su. 

A karshe dai Khalifa Muhammadu Sanusi na da mata hudu da ‘ya’ya goma sha uku, mata takwas, maza biyar kamar yadda alkaluma suka tabbatar.


Ammar M. Rajab ya rubuta mana ne daga Zariya, kuma zaku iya samunsa a ammarrajabonline@gmail.com

Post a Comment

0 Comments