Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Muna Murna Da Sakin El-Zakzaky, Inji Mazauna Unguwar Gyallesu

  Daga Hagu: Shaikh Ibraheem Zakzaky da Dan Uwansa Malam Abdulkadir Yaqoub zaune a gidansa  dake Gyallesu kafin a akai ga rushewa.  Daga M...

 

Daga Hagu: Shaikh Ibraheem Zakzaky da
Dan Uwansa Malam Abdulkadir Yaqoub zaune a gidansa 
dake Gyallesu kafin a akai ga rushewa. 


Daga Muhammad A. Dalhatu


- Idan Ya Zabi Ya Dawo Unguwarnan, Tabbas Muna Maraba


A makon da ya gabata ne Babban Editan MADOGARA ya yi tattaki zuwa Unguwar Gyallesu dake karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna domin jin ra’ayin mazauna Unguwar dangane da sakin da kotu ta yi wa Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya wanda aka fi sani da ‘yan Shi’a, Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Zeenat Ibrahim.

Sai dai a tattakin da Editanmu ya yi zuwa Unguwar Gyallesu inda Shehin Malamin ke zaune kafin a kama shi, ya tadda gidansa ya zama kufai, ba komai sai fili cike da ciyawa. Baya ga duba muhallin, Editanmu ya gana da wadansu ba’adin al’umma da suke zaune a Unguwar inda suka bayyana masa cewa tabbas suna mai matukar farin cikinsu da sakin Shehin Malamin da aka yi. “gaskiya na yi matukar farin ciki da sakinsa da kotu ta yi. Domin tabbas an zalunce sa. Kuma mutanen da suke adawa da shi a Unguwar nan suna yi ne ba don komai ba sai saboda bambancin akida, tabbas sun zalunce shi da karairayinsu, kuma Allah zai saka masa”, inji Abubakar Muhammad daya daga cikin mazauna Unguwar wanda ya kai shekaru 25 yana zaune a Unguwar.

Shi ko Magaji Musa wani mazauni Unguwar wanda ya ce yanzu shekarunsa kusan 40 a duniya ya bayyana mana cewa; “maganar gaskiya shi ne, Shaikh Zakzaky bai cutar da kowa a Unguwar nan ba. Bilhasalima mutum ne da ya san hakkin makwabtansa kuma yana saukewa. Akwai wadanda musamman a Unguwar nan wadanda ya hada da Dattijai, Tsoffi da Malamai wadanda Shehin Malamin yake girmama su har ma yana taimaka musu da kudi ko wani taimako idan ya taso, kowa ya sannan wannan komin kiyayyarka da shi. Hatta kofofin da aka sanya a Gyallesu da kudinsa aka sanya su”, ya jaddada mana.

A wani bangare na bayaninsa, wani matashi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana mana cewa;

“duk wanda ka ga yana maganar wai ba ya son wannan mutumin (Zakzaky) ya dawo Gyallesu, wallahi dan Izala ne ko Basalafe, a don haka ba abin mamaki bane don dan Izala ko Basalafe ya tsani Zakzaky saboda ya san Zakzaky shi ne shugaban Shi’a a Nijeriya. Ni iyayena a nan Unguwar suke zaune, nima haka, kuma wallahi ina kaunar Zakzaky saboda Allah”, ya jaddada.

Kazalika, mun samu tattaunawa da wani Dattijo wanda ya ce ba ya son a ambaci sunansa a rahoton, amma ya bayyana mana cewa yanzu shekarunsa fiye da 50, kuma ya dade a Unguwar a zaune, ya tabbatar mana da cewa; “tabbas a farko-farkon shekarar 2015 akwai hatsaniyar da aka samu a tsakanin wasu ‘yan iskan Unguwar da wasu da ba su da ra’ayin Malam Ibraheem inda suka tayar da fitina wanda su kuma mabiyan Zakzaky din suka maida martani domin kare Malaminsu, amma a ce Malam Ibraheem ba shi da hali mai kyau na zamantakewa wannan ba gaskiya bane, amma idan kana kiyayya da shi saboda wata manufa ta ka, to mutum zai iya fadin hakan. Amma mutum ne (Zakzaky) mai kyautatawa hatta ga wadanda ya san a Unguwar suna cutar da shi ne ma”, ya nusasshe.

Fatima Khalifa (ba asalin sunanta ba ke nan), ta bayyana cewa ita ta ji dadin sakin Shehin Malamin, domin a cewarta an zalunce shi; “kuma idan ya zabi ya dawo Unguwarnan, tabbas muna maraba da dawowarsa. Gaskiya ni a ra’ayina zan yi matukar farin ciki”, ta nanata.

KOTU TA SAKI EL-ZAKZAKY

Awatan jiya ne Babbar Kotun Jihar Kaduna a karkashin Mai Shari’a Gideon Kurada ta bayar da umarnin a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Zeenat Ibrahim, inda ta wanke su daga dukkan zarge-zargen da ake yi musu baki daya.

GANAWARSA DA WADANSU BA’ADIN ALMAJIRANSA

Bayan sakinsa da aka yi nan take tun a kotun a ranar Laraba, Shehin Malamin ya yi ganawar farko a karshen makon da aka sake shi da wadansu ba’adin almajiransa a Birnin Tarayya Abuja. Kuma tuni  hankali ya koma kan yadda zai dawo ya ci gaba da harkokinsa, inda ba a tantance ko a gidansa ne da aka rushe dake Unguwar Gyallesu zai dawo ya ci gaba da zama ba ko kuma zai sauya muhalli ne.

KISAN KIYASHI A ZARIYA

A Disambar shekarar 2015 ce aka kama Shehin Malamin da matarsa bayan kashe mabiyansa kusan dubu daya da da sojojin Nijeriya suka yi bisa zarginsu da tarewa shugaban sojoji na wancan lokaci, Tukur Burutai hanya, zargin da ‘yan shi’ar suka karyata, inda suka ce; “dama can an tsara afka musu tare da kashe su ne da kashe Malaminsu”.

KWAMITIN BINCIKEN KISAN KIYASHIN

Kwamitin binciken kisan kiyashin ‘yan shi’ar da gwamnatin Kaduna karkashin Gwamna Nasir El-Rufai ta kafa, ya tabbatar da cewa an bizne ‘yan shi’ar 347 a ramin bai daya a Unguwar Mando a Kaduna wadanda aka kashe a yayin da sojojin suka afka musu a Zariya, inda kwamitin ya nemi da a hukunta sojojin dake da hannu a wannan aika-aikar, shawarar da har yanzu gwamnatin ba ta aikata ko cewa uffan a kai ba.


No comments