Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da mutuwar mutum 60 sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar wadda ta kama mutane sama da 1,400. Kwamishi...
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da mutuwar mutum 60 sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar wadda ta kama mutane sama da 1,400.
Kwamishinan lafiyar Jihar Yakubu Danja ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da shugabannin kungiyar likitocin Nijeriya a birnin Katsina.
Danja ya ce yanzu haka gwamnatin na raba maganin yaki da cutar kyauta a asibitocin dake jihar domin dakile yaduwar cutar, tare da kuma shelar yadda jama’a za su kare kan su daga harbuwa da ita.
A makon jiya hukumomin jihohin Sakkwato da Zamfara sun sanar da yawan mutanen da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar da suka kai 53. 30 daga cikin su sun mutu ne a Jihar Zamfara, a yayin da 23 suka mutu a Sakkwato.
No comments