A ƙalla mutum 21 ne ake tunanin sun mutu ranar lahadi lokacin da wata gada ta karye a ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Jaridar Prem...
A ƙalla mutum 21 ne ake tunanin sun mutu ranar lahadi lokacin da wata gada ta karye a ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.
Jaridar Premium Times a Najeriya ta ruwaito cewa cikin mutanen har da wasu mutum 11 da suka nemi aikin soja ba a É—auke su ba.
Mazauna yankin sun bayyana cewa gadar ta karye ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Jaridar ta ruwaito cewa mutanen da suka rasu na tafiya ne daga Kano zuwa jihar Adamawa lokacin da lamarin ya faru.
BBC ta ce; dama dai an ba da rahoton cewa gwamnatin jihar Jigawa ta hana motoci bin hanyar da ta haÉ—a jihohin jigawa da Kano da yankin arewa maso gabashin Najeriya bisa lalacewar gadar dalilin ruwan sama.
Kawo yanzu hukumomin a jihar ba su ce komai ba game da hatsarin.
No comments