Nijeriya Ta Yi Asarar Zuba Jarin Da Ya Kai Dala Biliyan 50 - Buhari

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar ta yi asarar zuba jarin da ya kai Dala biliyan 50 a cikin shekaru 10 da suka gabata saboda rashin sake fasalin dokar man fetur da iskar gas din da ya rattabawa hannu akai wannan makon.

Yayin da yake jawabi wajen bikin sanya hannu akan dokar wanda aka yi a fadar sa da ya samu halartar shugabannin majalisun dokokin kasar da kuma ministoci, Buhari ya ce tsaikon da aka samu wajen yin sabuwar dokar ta haifar da matsala wajen ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.

Shugaban ya danganta matsalar da aka samu daga gwamnatocin da suka gabata wadanda suka kasa samar da yanayi mai kyau wajen amincewa da sabuwar dokar wadda ta kwashe kusan shekaru 20 a gaban majalisa.

Buhari ya ce sun fahimci cewar gwamnatocin da suka gabata na da masaniyar alherin dake tattare da sabuwar dokar wadda zata bada damar gudanar da harkokin man kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya, amma suka kasa mayar da hankali akai saboda wasu dalilai.

Shugaban ya ce tsaikon ya mayar da hannun agogo baya dangane da cigaban tattalin arzikin kasar ta hanyar zuba jari, inda yace a cikin shekaru 10 da suka gabata, Najeriya tayi asarar abinda ya kai Dala biliyan 50 daga yan kasuwar dake bukatar zuba jarin saboda rashin yin dokar.

Buhari ya ce wannan ya sa gwamnatin sa ta hada kai da majalisun tarayya guda biyu wajen ganin wannan mafarki ya tabbata, wanda ke cikin shirin gwamnatin sa na bude kofofin gudanar da harkokin man da samar da ayyukan yi da kuma kara yawan kudaden dake shiga aljihun gwamnati.

Daga bisani shugaban ya nada kwamitin da zai jagoranci aiwatar da dokar a karkashin karamin ministan mai Timipre Silva.

-Rfi Hausa

Post a Comment

0 Comments