Rafali Ya Zaro Bindiga Yayin Da Faɗa Ya Ɓarke a Filin Ƙwallo


Wani Rafalin kwallon ƙafa ya ɗauki hankula bayan da ya zaro Bindiga a yayin da rikici ya ɓarke a filin ƙwallo.

Fenareti ce da aka ƙi bayarwa ta jawo hayaniyar, wadda tasa Rafalin ya fitar da bindiga ya riƙa yawo da ita a cikin fili.

Rahotanni sun ce daya daga cikin 'yan wasan ne ya zagi Rafalin da miyagun maganganu wanda hakan ya fusata shi ya zaro bindigar.

Rahotanni sun ce Rafalin ya yi hakan ne domin ya bai wa kansa kariya daga fusatattun 'yan wasan da magoya bayansu.

Lamarin ya faru ne a wani filin ƙwallo na ƙasar Honduras.
Post a Comment

0 Comments