Real Madrid Ta Sanya Yuro Miliyan 180 A Kan Mbappe

 


Real Madrid ta kara yawan kudin da ta taya dan wasan PSG Kylian Mbappe zuwa Yuro miliyan 180.

Real dai ta shirya biyan Yuro miliyan 170 da kuma karin garabasa na miliyan 10 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Hakan ya zo daidai da abin da PSG din ta kashe wajen dauko dan wasan daga Monaco a shekarar 2017.

Tun da farko a wannan makon, daraktan wasannin PSG ya yi fatali da tayin da Real Madrid ta yi na miliyan 160 na kudin Yuro, yana cewa kudin ya yi kadan ainun, inda ya ce sai an biya Yuro  miliyan 220 za a saki Mbappe.

A watan Yunin shekara mai zuwa ne kwantiragin Mbappe zai kare da kungiyarsa ta PSG.


Post a Comment

0 Comments