Wasu magoya bayan jam'iyyar PDP a karkashin kungiyar 'PDP Frontliners' sun nemi shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus da ya yi murabus.
Membobin kungiyar sun gabatar da wannan bukata ne a wani taron manema labarai a Kaduna ranar Lahadi.
Sun nuna bacin ransu cewa duk da rashin rashin katabus din da ya yi a shugabancin PDP, Secondus ya fi son ci gaba da zama a kan kujerar fiye da ba da damar canje-canjen da za su shirya jam'iyar don samun nasarar zaɓe a 2023.
Membobin Ƙungiyar ta PDP, karkashin jagorancin Alhaji Hussein Mohammed a matsayin Shugaban kasa, Mista Moses Abidemi, Sakatare da Mista Dan Okafor, Sakataren Yada Labarai, sun nuna mamakin yadda Secondus ya ki yin murabus duk da gazawar da ya yi.
0 Comments