Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rochas Okorocha Zai Gina Jami'ar Musulunci A Garin Daura

Daga Muhammad A. Dalhatu  MADOGARA ta labarto cewa; tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina Jami'ar ...Daga Muhammad A. Dalhatu 

MADOGARA ta labarto cewa; tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina Jami'ar Musulunci a garin shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Daura ta jihar Katsina. 

Okorocha, wanda yake Sanata ne a yanzu, kuma jigo a jam'iyyar APC, ya bayyana cewa zai gina Jami'ar ne a karkashin Gidauniyyar Rochas Okorocha. 

Tsohon gwamnan a kwanan nan Masarautar Daura ta ba shi sarautar 'Maga Alherin Kasar Hausa', wanda Sarki Umar Faruk ya ba shi. 


Isa Halidu, wanda ya wakilci Okorocha a wani taro a ranar Asabar a Daura on Saturday, ya ce daliban da za a dauka a Jami'ar ba za su biya kudin makaranta ba da na dakunan kwana ba a Jami'ar. 

"Saboda Sarkin Daura ya bani sarautar gargajiya, zan bada tukwuici, wanda ba za a ta6a mantawa da shi ba. Zan gina Jami'ar Musulunci mai dauke da kayayyakin zamani a karkashin gidauniyyar Rochas Okorocha kuma zan kaddamar da shi da kaina a garin Daura", inji shi. 

Ya ce zai yi hakan ne saboda yadda masarautar da ma jihar Katsina baki daya suka nuna mishi kauna. 

Okorocha ya ce gidauniyyarsa ta gina makarantu kuma yana gudanar da ayyukan ci gaba da dama a wadansu jihohin. Domin haka zai yi wannan aikin a Daura ne domin biyan shugaba Buhari abin da yake yi wa Nijeriya. 

No comments