Sabuwar Fuskar Taliban: Ta Bayyana Yadda Za Ta Mulki Afghanistan


Daga Muhammad A. Dalhatu

Kungiyar Taliban ta gudanar da taron manema labarai a karon farko tun bayam hambare gwamnatin Ghani a Afghanistan, inda ta yi shelar kawo karshen yakin da kasar ta shafe shekaru 20 tana tafkawa tare da sanar da yi wa kafatanin masu adawa da ita afuwa.


A yayin taron manema labaran, Kakakin kungiyar Zabihulla Mujahid ya yi alkawarin bai wa mata damar gudanar da ayyuka bisa tsarin addinin Musulunci, sabanin yadda matan suka kasance a karkashin kungiyar a fiye da shekaru 20 da suka gabata.


Mujahid ya kara da cewa nan gaba kadan za su kafa sabuwar gwamnati, sai dai bai yi cikakken bayani kan yadda sabuwar gwamnatin za ta kasance ba, amma ya ce za a baiwa dukkanin bangarori dama.


Jim kadan bayan kammala taron manema labaran, mataimakin shugaban kungiyar Mullah Abdul Ghani Baradar wanda ya taka rawa wajen kafuwarta ya isa Kandahar, tsohon babban birnin Afghanistan a zangon farko na mulkin ‘yan Taliban fiye da shekaru 20 baya.

Yayin tsokaci kan sauyin da aka samu a Afghanistan, jim kadan bayan taron gaggawa na ministocin waje na kasashen Tarayyar Turai, babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turan Josep Borell ya ce dole su tattauna da kungiyar Taliban da a yanzu ke rike da madafun iko, la’akari da nasarar da suka samu, bayan rushewar gwamnatin da kasashen yamma ke marawa baya.

Post a Comment

0 Comments