Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Saudiya Ta Fara Biyan Diyyar Ma'aikatan Lafiyar Da Korona Ta Kashe

  Kasar Saudi Arabia ta fara biyan diyya ga iyalan jami’an kiwon lafiyar ta da suka mutu sakamakon yaki da annobar korona, inda kowanne mutu...

 


Kasar Saudi Arabia ta fara biyan diyya ga iyalan jami’an kiwon lafiyar ta da suka mutu sakamakon yaki da annobar korona, inda kowanne mutum guda zai karbi Dala dubu 133 kamar yadda RFI Hausa suka labarto.

A watan Oktobar bara gwamnatin kasar tace zata biya Riyal dubu 500 ga Yan uwan kowanne ma’aikacin lafiyar da ya rasu sakamakon harbuwa da cutar, cikin su harda jami’an asibitin gwamnati da na masu zaman kan su da na fararen hula da kuma soji.

Sanarwar gwamnatin tace matakin zai fara aiki ne daga ranar 2 ga watan Maris din shekarar 2020 da a hukumance aka tabbatar da samun cutar a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Saudiya yace matakin wani nuna godiya ne ga gudumawar da jami’an lafiyar suka bayar domin kare lafiyar jama’ar dake zama a Masarautar.

Babu dai adadin jami’an kiwon lafiyar da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar koronar a kasar dake da dubban jami’an kiwon lafiyar da suka fito daga kasashen waje.

Gwamnatin kasar ta kara kaimi wajen yiwa jama’a allurar rigakafin a kokarin da take na bude kofofin ta ga baki Yan yawon bude ido da masu zuwa Umrah da kuma wasanni.

Ma’aikatar lafiyar tace akalla allura miliyan 29 aka gabatarwa mazauna kasar wanda ke dauke da mutanen da yawan su ya kai miliyan 35.

Gwamnatin Saudi Arabia ta sanya dokar tilastawa duk wani mai bukatar shiga gine ginen gwamnati ko na kamfanoni ciki harda makarantu gabatar da shaidar dake nuna cewar an masa rigakafin.

Akalla mutane sama da dubu 8,300 suka mutu a Saudiyar daga cikin dubu 533 da suka harbu da cutar.


No comments