Shugaba Buhari Ya Gana Da Sheikh Ɗahiru Bauchi A Abuja


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, a fadar gwamnati ta Aso Rock Villa a jiya Laraba.

Ganawar ba ta rasa nasaba da kisan gilla da aka yi wa Musulmai da suka halarci zikirin sabuwar shekara a gidan Sheikh Dahiru Bauchi a hanyar su ta komawa jihohin su a daidai ƙauyen Rukuba dake Jos ta Arewa kamar yadda Hausa Daily Times ta labarto. 
 
A hira da ƴan jaridu a Abuja, Shehin Malamin, ya ce sun bar komai a hannun gwamnati amma in ta kasa ɗaukar mataki su za su san abun yi.

Post a Comment

0 Comments