Shugaba Buhari Zai Cefanar Da NNPC

 


Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa za a rusa babban kamfanin kasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC.

Sai dai ya ce za a maye gurbinsa da wani kamfanin mai zaman kansa.

Wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.

Ministan albarkatun man fetur Timipreye Silver ne zai jagoranci wannan kwamitin.


Post a Comment

0 Comments