Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Rasha Putin Ya Soki Amurka Da Turai Kan Kwashe 'Yan Afghanistan

 Shugaban Rasha Vladimir Putin ya soki Amurka da ƙasashen Yamma saboda sun buƙaci ƙasashen Asiya su ɗebi 'yan gudun hijirar Afghanistan ...


 Shugaban Rasha Vladimir Putin ya soki Amurka da ƙasashen Yamma saboda sun buƙaci ƙasashen Asiya su ɗebi 'yan gudun hijirar Afghanistan ba tare da biza ba.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito Putin na bayyana haka ne a wurin wani taron siyasa.

Ya ce: "Abokan aikinmu na Yamma na son ƙawayenmu na Nahiyar Asiya su karɓi 'yan gudun hijira (na Afghanistan) har sai sun gama sama musu biza a Amurka da sauran ƙasashe.

"Shin hakan na nufin za su iya aika su zuwa waɗannan ƙasashe maƙotanmu ba tare da biza ba - amma su ba sa so su karɓe su ba tare da bizar ba?"

Amurka na ci gaba da tattaunawa da wasu ƙasashe don su bai wa 'yan Afghanistan mafaka ta ɗan lokaci.

Duk da cewa Rasha na karɓar 'yan ƙasashen Asiya tsofaffin mamba a Tarayyar Soviet ba tare da biza ba amma ya koka cewa 'yan bindiga ka iya amfani da wannan damar su shiga ƙasarsa.


-BBC Hausa

No comments