Rundunar sojin Nijeriya sun fafataki ƴan bindiga daga ginin wata makaranta da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara a wasu hare-hare...
Rundunar
sojin Nijeriya sun fafataki ƴan bindiga daga ginin wata makaranta da ke karamar
hukumar Shinkafi a jihar Zamfara a wasu hare-haren sama.
BBC
sun ce hare-haren da suka kai da jiragen yaƙi sun yi luguden wuta a yankunan
Zangon Dammaka da Jajaye maboyar wani fitaccen ɗan bindiga Kachalla Haru da
yaransa.
Ɗaya
daga cikin dakarun hadin-gwiwar da suka kai harin a Zamfara ya shaidawa Jaridar
PRNigeria cewa sun yi nasara a dukkanin samamen da suka kai a karshen mako.
A
cewar dakarun anyi nasarar kashe ƴan bindiga da dama da lalata makamansu.
Sannan an lalata dazukan da suke ɓuya a Sububu. Kuma an yi nasara ba tare da
shafar farar-hula ba.
Wata
majiya ta tabbatarwa PRNigeria cewa an kashe sama da ƴan bindiga 50 da lalata
makamansu da babura a kauyen Gidan Rijiya.
No comments