Daga Wakilinmu A ranar Juma’ar da ta gabata ne 6 ga Agustan 2021, wasu tunzurarrun matasa suka auka wa Alaramma Malam Ali da duka da sar...
Daga Wakilinmu
A ranar Juma’ar da ta gabata ne 6 ga
Agustan 2021, wasu tunzurarrun matasa suka auka wa Alaramma Malam Ali da duka
da sara. Daga karshe suka kwara masa fetur suka banka masa wuta, nan take rai
ya yi halinsa.
Lamarin ya faru ne a wani gari da
ake mira Babaldu dake karamar Hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya
gano cewa, Malam Ali ya ari Babur din abokinsa Alaramma Malam Yusuf mai Manja
ya tafi gona da shi, sai mashin din ya ba shi matsala a garin na Babaldu, sai
Malam Ali ya bada ajiyarsa ya hau mota ya karasa gonarsa.
Bayan Malam Ali ya dawo daga gona da
sakaliyar la’asar ana ruwa. Ya zo daukar mashin dinsa kawai sai wani mutum ya
yi masa ihun barawo. Nan da nan wasu fusatattun matasa suka yo kansa da duka da
sara. Nan take suka kashe shi, suka banka wa gawarsa wuta. Daga bisani suka
tura mashin din nasa zuwa wajen ‘yan sanda.
“Ni ba barawo bane. Ni dan Birnin
Kudu ne. Ni ne Sakataren masu zazzaba shinkafa a garin Sara, ga wayata ku kira
ku tambaya”, inji Marigayi Alaramma Malam Ali lokacin da suka fara dukansa. Amma
duk da haka fusatattun matasan nan suka ce karya yake, suka ci gaba da dukansa
har ya rasu.
“mun kama barawon babur mun kashe
shi, mun kone shi kurmus, ga mashin din da ya sato, kuma ko gobe muka kara
kamawa za mu kashe”, inji daya daga cikin makasan.
An gano cewa Malam Ali ne aka kashe
a Babaldu a ranar Talatar da ta gabata bayan rashin dawowarsa gida tun ranar
Juma’a. Sai aka samu labarin cewa wanda aka kashe din nan a Babaldu mashin
dinsa yana wurin ‘yan sanda.
Mai mashin din, Alaramma Malam Yusuf
mai Manja ya tafi wurin ‘yan sanda. Yana zuwa kuwa ya ce lallai wannan mashin
dinsa ne. A nan take ta tabbata cewa Malam Ali ne aka kashe a Babaldu.
Da yake zantawa da manema labarai,
DSP Lawal Shi’isu, wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda
ta jihar Jigawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce; “yanzu haka mun kama
mutum kusan 20, kuma suna sashen binciken manyan laifuka na CID ana bincike a
kansu, kuma da zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da su a gaban kotu don
su girbe abin da suka shuka”.
Bayan samun wannan tabbaci ne, ‘yan’uwa
da abokan arziki suka isa wurin da aka bizne shi a Babaldu suka tono shi suka
dawo da abin da ya rage na jikinsa aka shirya shi, kamar yadda adddinin
Musulunci ya tanada aka yi masa sallah a babban Masallacin Biirnin Kudu aka
raka shi makwancinsa.
Wannan al’amari dai ya sosa zuciyar
al’ummar wannan yanki na Birnin Kudu gaba daya, inda ya zama shi ne abin da ake
tattaunawa a wannan lokaci, kuma kowa yake yi wa dan’uwansa jaje.
“Yaushe ne jama’a za su daina daukar
doka a hannunsu, mutane su rika kashe mutane haka kawai babu bincike. Kowa ya
zama Alkalin kansa, mutane suna zaune kamar babu hukuma?” inji daya daga cikin
iyalan mamacin.
Wasu jama’a kuwa sun dora alhakin a
wuyan Hukuma, domin ita ce alhakin kula da rayuka da dukiyoyin al’umma suka
rataya a wuyanta.
Yanzu dai jama’ar wannan yanki na
Birnin Kudu sun zuba ido su ga irin hukuncin da za a zartarwa ilahirin wadanda
ake zargi da hannu wurin kisan wannan bawan Allah.
Malam Ali dai Alaramma ne, manomi,
kuma dan kasuwa. An ce ya rubuta Kur’ani sau biyu da hannunsa. Ya rasu ya bar
mata daya da ‘ya daya.
Kwafowa daga Jaridar Almizan ta wannan makon.
No comments