Kimanin makonni hudu ke nan da wata babbar kotun Kaduna ta saki tare da wanke Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky...
Kimanin makonni hudu ke nan da wata
babbar kotun Kaduna ta saki tare da wanke Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya,
Shaikh Ibraheem Zakzaky, da matarsa Malama Zeenah Ibrahim, sai dai har yanzu ba
su kai ga fita kasashen waje domin neman magani saboda jami’an tsaro na rike
fasfo dinsu.
Ibrahim Musa, shugaban sashen yada
labarai na Harkar Musulunci, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya
fitar, inda ya ce ba a san fasfo din ko yana hannun wacce hukuma bane, domin
hukumar liken asiri ta NIA da ta fararen kaya DSS duka sun ce ba su rike da
fasfo din mutanen biyu.
Sanarwar ta kara da cewa abin da ya
bayyana shi ne lokacin da babbar Kotun Kaduna ta yarje wa Shaikh Zakzaky da
matarsa fita neman magani Indiya a shekarar 2019, jami’an tsaro sun karbe
takardun shaidar tafiyarsu.
Wa aka bai wa takardun? Wannan
tambayar da kyar za ta samu amsa ganin cewa an dauki lokaci da faruwar abin tun
2019.
Sai dai mabiya na tambayar ko wani
babban mai mukami ne ke neman amfani da wannan damar ya kara yi masu daurin
talala a cikin kasar, a cewar sanarwar Ibrahim Musa mutane da dama na hasashen
haka.
“Muna amfani da wannan damar domin sanar da mutane kimanin shekara shida, sakamakon rahoton da aka fitar na lafiya a kansu ya nuna cewa suna cikin yanayin rashin lafiya sosai, abin da kotun ta duba ke nan ta ba su damar fita neman magani wanda gwamnati ta hana hakan a 2018”, in ji sanarwar
No comments