Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Taliban Ta Yi Bikin Ficewar Amurka Daga Afghanistan

  Mayakan Taliban sun yi bikin murnar karbe iko da gwamnatin Afghanistan baki daya bayan Amurka ta kammala ficewa daga kasar a yau Talata, i...


 

Mayakan Taliban sun yi bikin murnar karbe iko da gwamnatin Afghanistan baki daya bayan Amurka ta kammala ficewa daga kasar a yau Talata, inda suka yi ta harbe-harben bindiga a sararin samaniya.

A hukumance, Amurka ta kawo karshen yaki mafi dadewa da ta yi tarihi, domin kuwa ta shafe kimanin shekaru 20 a Afghanistan.

Dakarun Amurka sun fice daga filin jiragen sama na birnin Kabul, inda suka shafe tsawon kwanaki suna sanya ido kan kwashe jama’ar da ke son ficewa daga Afghanistan.

Sama da mutane dubu 123 ne aka kwashe daga kasar ta Afghanistan domin tsoron mulkin Taliban.

Jim kadan da ficewar sojojin Amurka, mayakan na Taliban sun mamaye harabar filin jiragen sama na birnin Kabul tare da harbe-harben bindigogi domin nuna murna.

A yayin jawabinsa, mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid ya shaida wa manema labarai cewa, wannan nasarar da suka samu ta Afghanistan ce.

Kazalika ya ce, wannan nasarar wata manuniya ce da ke matsayin darasi ga manyan kasashe masu mamayar kananan kasashe.


No comments