Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tarihin Yusuf Buhari Da Habibiyarsa Zahra Bayero

  Yau dan shugaban kasa Muhammadu Buhari ke auren habibiyarsa kuma gimbiyar Masarautar Bichi wato Zahra Nasir Ado Bayero. Yusuf  mai shekaru...

 Yau dan shugaban kasa Muhammadu Buhari ke auren habibiyarsa kuma gimbiyar Masarautar Bichi wato Zahra Nasir Ado Bayero.

Yusuf  mai shekaru 27, shi ne da namiji daya tilo ga shugaba Buhari da uwargidansa A’siha ta haifa masa.

Ita kuwa Zahra ‘yar shekaru 20, ‘ya ce ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero wanda kuma ke shugabantar kamfanin layin sadarwa na 9mobile a Najeriya.

Yusufa dai, ya kammala karatun digirinsa na farko a jami’ar Surrey da ke Birtaniya, yayin da amaryarsa ke kan karantar ilimin zanen gine-gine a wata jami’a a Birtaniyar.

Ana sa ran manyan baki daga sassan duniya su halarci daurin auren na yau a babbar Masallacin Juma’a na garin Bichi.

Tuni aka girke jami’an tsaro a daidai lokacin da ake shirin daura auren da misalin karfe 1 da rabi na rana agogon Najeriya.

No comments