Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tashar Tambari Hausa Ta Sanya Wa Hedikwatarta Sunan Fitaccen Danjarida Halilu Ahmed Getso

Tashar Tambarin Hausa ta maye gurbin sunan Cibiyar zuwa sunan fitataccen mai yada labarai kuma shahararren dan jarida Halilu Ahmed Getso a r...


Tashar Tambarin Hausa ta maye gurbin sunan Cibiyar zuwa sunan fitataccen mai yada labarai kuma shahararren dan jarida Halilu Ahmed Getso a ranar Lahadi, 8 ga watan Augusta 2021.

Cibiyar yada labaran ketare da harshen hausa ta farko wacce take jihar Kano a Arewacin Najeriya ta maye gurbin sunanta zuwa sunan fitaccen mai yada labarai kuma dan jarida Alhaji Halilu Ahmed Getso dan nuna gamsuwa da jinjina irin gudunmawar daya bayar akan tafi da aikin jarida da yada labarai a Najeriya.

Alhaji Ibrahim Makama wanda shine shugaba kuma wanda ya kirkiri tashar ya bayyana haka ne a wajan tattaunawa ta masu hannu da tsaki a tashar dake jihar Kano. Ya kara da cewa wannan shawara da aka yanke ta sauya sunan cibiyar yada labaran ketare da harshen Hausa zuwa sunan Alhaji Halilu Ahmed Getso ya samu tushe n daga irin gudunmawar daya bayar a aikin jarida shekara hamsin baya da suka wuce.

Alhaji Halilu Ahmed Getso ya bayyana cewa yayi mamaki da kuma bazata na faruwar hakan, kuma ya kara da cewa wannan wani babban cigaba ne a rayuwarsa na mai yada labarai kuma dan jarida.

Ya kara da cewa a wannan yanke shawara da shugaban tashar yayi yasa ya hangi lokacin da yake aiki a Radio Nigeria da kuma BBC Hausa.

Alhaji Halilu ya gargadi kananan yan jaridu da masu tasowa akan kar su fifita kudi a yayin da suke gudunar da aikinsu.

Tashar Tambarin Hausa tana gudanar da gwaji a jihar Kano dake Arewacin Najeriya kuma za'a kaddamar da Tashar don ta fara gudanar da yada labari da kuma shirye-shirye.

No comments