Wutar Daji Ta Kashe Mutane 42 A Algeria


Wutar dajin dake ci gaba da ci a kasar Algeria ba tare da kaukautawa ba tayi sanadiyar kashe mutane 42 cikin su harda sojoji 25 dake aikin agaji domin ceto mutanen da suka makale a gidajen su.

Hotunan da aka yada ta kafar sada zumunta sun nuna yadda harsunan wutar ke lakume itatuwa dake gandun dajin Yankin Kabylie daga gabashin birnin Algiers.

Shugaban kasa Abdelmajid Tebboune ya aike da sakon ta’aziyyar sa ga ‘yan uwa da iyalan wadanda suka mutu ta kafar twitter, musamman sojojin da suka sadaukar da rayukan su domin shawo kan gobarar a Yankin Bejaiea da Titi Ouzou.

Tebbounce ya bayyana kaduwar sa da mutuwar sojojin 25 lokacin da suke kokarin ceto fararen hula kusan 100 daga wutar a tsaunukan Bejaiea da Titi Ouzou.

Ma’aikatar tsaron kasar tace sojojin sun yi nasarar ceto mutane 110 cikin su harda da mata da yara kanana, yayin da 14 daga cikin dakarun suka samu raunuka.

Firaminista Aimene Benaabderrahmane yace fararen hula 17 suka mutu a Tizi Ouzou da Setif.

Kasar Tunisia ta shiga cikin jerin kasashen duniya dake fama da wutar daji da suka hada da Girka da Turkiya da Cyprus da kuma Yammacin kasar Amurka.


-RFI Hausa

Post a Comment

0 Comments