Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Kotu Ta Dakatar Da El-Rufai Daga Binciken Zanga-zangar Da Kungiyar Kwadago Ta Yi A Kaduna

Daga Ammar M. Rajab Kotun ma’aikata ta kasa (NIC) dake zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta dakatar da kwamitin  bincike da Gwamna Nasir El-Ruf...


Daga Ammar M. Rajab

Kotun ma’aikata ta kasa (NIC) dake zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta dakatar da kwamitin  bincike da Gwamna Nasir El-Rufai ya kafa domin ya yi bincike tare da kawo shawarwarin yadda za a hukunta wadanda suka shiga cikin yajin aikin  kwanaki biyar da kungiyar kwadago ta kasa wato NLC ta yi kwanakin  baya a jihar ta Kaduna.

Kotun a hukuncin da ta yanke, wanda mai shari’a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae ya jagoranta, ya dakatar da membobi tara na kwamitin a karkashin shugaban kwamitin kuma tsohon Alkali a kotun Abuja, Mai Shari’a Ishaq Bello, da “gudanar datambayoyi, bayar da shawara kai, bincike, ko kuma ci gaba  da bincike a kai, ko bayar da shawara a kai, ko kuma samo shaida a kai, ko ta hanyar tilasta halarta gabanta (ta hanyar aikawa shaida sammaci ko shaidar kamu, bisa kowanne irin  dalili),” ga membobin kungiyar {wadago ko kuma wadansu membobin al’umma domin gabatar da dukkanin wata shaida a gabanta dangane da yajin aikin.

Kotun ta kara bayar da umurni kan cewa; “wannan umurnin wucin gadi na hana wanda ake kara na 3 (kwamitin bincike) daga gudanar da aikin da aka sanya shi bisa sharudan da aka gindaya masa mai kwanan wata 6 ga Yulin 2021, kamar yadda wanda ake kara na 1 a karkashin dokokin bincike (Cap 34) da kuma dokokin jihar Kaduna ta Nijeriya, har sai an tabbatar da ikirarin wanda ya shigar da kara yana neman wannan umurnin”, inji kotun.

Kazalika, “umurnin wucin gadin ya hana wadanda ake kara, aikatawa da kansu, ko sanya ma’aikatansu, wakilansu, da masu zaman kansu ko kuma akasin haka, daga gayyata, ganowa, bincika, samar da shaidu, sammaci, takaddama, bayar da umurni kan tursasawa membobi na 1 da ke adawa domin halartar duk wani zaman sauraro, taro, "gwaji", tambayoyi, bincike, zaman kwamitin, da duk yadda aka kira zaman, dangane da, ko kuma an haɗa shi da batun da mai kara na daya ya shigar kan yajin aikin gargaɗi da suka shiga a ranar 16 ga Mayu 16, 2021 , zuwa 19 ga Mayu 2021, da kuma dukkanin ayyuka da batutuwan da suka faru a yayin yajin aikin, har sai lokacin da masu shigar sun tabbatar da ikirarinsu”, kotun  ta umurta.

Har wala yau kotun ta nemi da a mika wannan hukuncin kotun ga gwamna El-Rufai, BabbanAttoni na jihar Kaduna, da kuma kwamitin da dukkanin membobin da aka shigar da kara gaban kotun kan wannan batun ta hanyar gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Mai Shari’a Obaseki-Osaghae ya dage shari’ar har zuwa 30 ga watan Satumbar shekararnan.

Wannan umurnin ya biyo bayan karar da kungiyar NLC, shugabanta, Kwamared Ayuba Wabba, mataimakinsa, Kwamared Joe Ajaero da kuma shugaban NLC ta jihar Kaduna, Kwamared Ayuba Sulaiman, suka shigar a karkashin lauyansu, Femi Falana, SAN.

Baya ga gwamna El-Rufai, Attoni na Kaduna, da kuma kwamitin binciken da aka sanya a matsayin wadanda ake kara na  1 zuwa na 3, sauran wadanda aka shigar kara sun hada da membobin kwamitin binciken, Mai shari’a Bello, AVM Rabiu Dabo, Eyo. O. Ekpo, Joan Jatau-Kadiya, Chom Bagu, Dr. Nasirudeen Usman, Malam Mohammed Aliyu, Mr. Daniel Enwelum, da kuma Sakataren kwamitin Musa Kakaki.

Masu gabatar da karar a cikin takardar bayanan da suka gabatar mai shafuka shafuka 56, wanda Kwamared Benson Upah, Shugaban yada labarai da hulda da jama'a na NLC, ya nemi kotun da ta dakatar da kafa kwamitin domin tabbatar da adalci.

Sun shaidawa kotun cewa NLC da shugabanninta sun samu rashin jituwa na tsawon lokaci da gwamnatin jihar Kaduna; “bisa manufofin adawa da ma’aikaci; bada izini ba tare da bin ka’idar doka, da kuma ba da sanarwar cike gurbin aiki ba tare da bin doka ba; tare da yin ritayar dole ga ma’aikatan da suke mataki na 14 zuwa sama”, inji su. 


No comments