Daga Muhammad A. Dalhatu ‘Yan bindiga sun samu nasarar kai hari a kwalejin horar da jami’an soji ta Kaduna wato NDA, inda suka kashe jami’...
Daga Muhammad A. Dalhatu
‘Yan bindiga sun samu nasarar kai hari a kwalejin horar da jami’an soji ta Kaduna wato NDA, inda suka kashe jami’an soji guda biyu, suka kuma yi awon gaba da wani babban jami’in kwalejin mai mukamin Manjo.
Ganau sun bayyana cewa ‘yan bindigar da suke da yawan gaske, sun kai farmaki ne a Kwalejin da ke kan titin filin jirgin sama a Afaka da ke cikin karamar hukumar mulki ta Igabi ne da sanyin safiyar ranar Talata.
Haka kuma sun bayyana cewa maharan suna sanye ne da kakin soji, inda suka sha karfin masu gadi, sannan suka dumfari gidajen jami’an sojin da ke cikin kwalejin.
Baya ga wadanda aka kashe da kuma wanda aka sace, an raunata da dama a harin, wanda a halin yanzu suke samun kulawa a Asibitin cikin Kwalejin kamar yadda bayanai suka tabbatar.
Babbar kwaleji ta horar da jami’an soji ta Kaduna, tana kusa da kwalejin horar da dabarun aikin gona ta gwamnatin Tarayya, inda a watannin baya ‘yan bindiga suka kai hari a ranar 11 ga watan Maris, suka kuma sace dalibai 39.
To sai dai an sako daliban bayan sun kwashe tsawon kwanaki 50 a hannun ‘yan bindigar, biyo bayan shiga tsakani na tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo, da Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gummi.
No comments