Ƙungiyar likitoci ta Nijeriya, NARD ta ƙi amincewa da tayin da gwamnatin Tarayya ta yi mata da zimmar ta janye yajin aikin da take yi yanzu ...
Ƙungiyar likitoci ta Nijeriya, NARD ta ƙi amincewa da tayin da gwamnatin Tarayya ta yi mata da zimmar ta janye yajin aikin da take yi yanzu haka kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Shugaban ƙungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa, ne ya tabbatar da hakan a yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron da suka yi da wakilan gwamnatin ranar Lahadi a Abuja.
Dr Uyilawa ya ce sun ƙi saka hannu kan yarjejeniyar ce saboda akwai sakin layin da ba a fayyace musu ba duk da cewa babbar ƙungiyar likitoci ta NMA ta ƙulla yarjejeniyar da gwamnati.
Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne likitocin suka shiga yajin aikin na sai baba ta gani domin neman a biya musu buƙatunsu.
Ministan Kwadago Chris Ngige ya miƙa batun hannun Kotun Ɗa'ar Ma'aikata domin ɗaukar mataki, inda rahotanni ke cewa gwamnati na son ta dakatar da biyan albashin likitocin da ke yajin aikin.
No comments