Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga 9 ne suka mutu sakamakon wani kazamin rikici da ya barke a tsakaninsu a wani kauye da ke karama...
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga 9 ne suka mutu sakamakon wani kazamin rikici da ya barke a tsakaninsu a wani kauye da ke karamar hukumar Giwa ta jihar.
Samuel Aruwan, wanda shi ne kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa wani kasurgumin dan bindiga da ake wa inkiya da Godon Mota ne ya kutsa da shi da tawagarsa kauyen Garke a Larabar da ta gabata, kuma nan ne rikici tsakanin abokan hamayyar ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda 9.
Aruwan ya ce har yanzu ba a tantance ummul’aba’isin rikicin na su ba, amma ana zargin ba zai rasa nasaba da rabon kudin fansa da suka tara ba.
Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya na fama da ayyukan ‘yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa.
No comments