Hukumar kare hakkin Bil Adama a kasar Habasha ta bayyana cewar 'yan bindiga sun kashe mutane sama da 210 a Yankin 'Yammacin kasar ...
Hukumar
kare hakkin Bil Adama a kasar Habasha ta bayyana cewar 'yan bindiga sun kashe
mutane sama da 210 a Yankin 'Yammacin kasar abinda ya haifar da daukar fansa kamar yadda RFI Hausa ta labarto.
Hukumar
tace mazauna yankin da aka kashe mutanen ne suka shaida mata yadda Yan bindigar
suka kashe wadannan fararen hula 210 a harin da aka kai ranar 18 ga watan nan,
bayan janyewar jami’an tsaro daga wani sashe na yankin Oromia, daya daga cikin
yankunan da ake fama da tashin hankali a cikin kasar.
Shaidun
gani da ido sun ce Yan bindigar na alaka da kungiyar neman ‘yancin Oromia ta
OLA, wadda ake zargi da yawan hare haren da ake samu a yammaci da kuma kudancin
kasar Habasha.
Hukumar
kare hakkin Bil Adamar tace kisan ya sanya mazauna yankin mata da yara yin
kaura zuwa yankunan dake makotaka da su domin kaucewa harin daukar fansa a
rikicin dake da nasaba da kabilanci wanda kafin wannan yayi sanadiyar kashe
mutane 60.
Kungiyar
OLA ta fice daga cikin OLF wadda jam’iyyar siyasa ce dake ta kwashe shekaru da
dama tana gudun hijira a kasar waje kafin hawa karagar Abiy Ahmad a shekarar
2018 wanda ya bata umurnin dawowa gida.
Gwamnatin
Abiy na zargin OLA da aikata kisan gilla da dama akan yan kabilar Amhara, wadda
itace kabila ta biyu mafi yawa a kasar, zargin da kungiyar tayi watsi da shi.
No comments