Marigayiya Hannatu Muhammad A jiya ne aka yi wa daya daga cikin wadanda masu garkuwa da jama’a suka sace a Unguwar Zangon Shanu Samaru sutur...
![]() |
Marigayiya Hannatu Muhammad |
A jiya ne aka yi wa daya daga cikin wadanda masu garkuwa da jama’a suka sace a Unguwar Zangon Shanu Samaru sutura bayan an tsinto gawarta a daji.
Wacce suka kashe ita ce Hannatu Muhammad, Masaniyar magani, kuma ma'aikaciya a Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU Zariya.
Maharan sun sace ta ne tare da 'yan'uwanta biyu da kuma wata mutum a Juma'ar da ta gabata 27 ga watan Agustan 2021.
Mutanen kauyen da masu garkuwa da jama’ar suka yar da gawar ta ne suka sanar cewa akwai gawa, shi ne rundunar 'yan bijilante da rakiyar jami'an tsaro na gwamnati suka je suka dauko ta.
No comments