BBC Hausa ta labarto cewa; 'yan bingida a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun kai hari kauyen Adabka da ke karamar hukumar Bukku...
BBC Hausa ta labarto cewa; 'yan bingida a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun kai hari kauyen Adabka da ke karamar hukumar Bukkuyum tare da sace dagacin yankin Alhaji Nafi'u Shehu.
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa jaridar The PUNCHcewa da misalin karfe 12 da rabi na ranar Asabar ne 'yan bindigar suka dirarwa fadar dagacin tare da masu yi masa hidima.
A cewarsa bayan sace dagacin sai da suka dauki sa'o'i a kauyen suna abin da suka ga dama.
"Abin mamaki ne, yadda 'yan bindiga suka shiga har fadar mai martaaba da masu yi masa hidima ba su saci kowa ba bayansu kuma ba su kashe kowa ba. Mun yi matukar kaduwa, mutane suka yi ta gudun tsira da ransu lokacin da suka ga 'yan bindigar dauke da AK-47 amma ba su taba kowa ba.... in ji mutumin da ya ga faruwar lamarin".
Abin mamaki ne, yadda 'yan bindiga suka shiga har fadar mai martaaba da masu yi masa hidima ba su saci kowa ba bayansu kuma ba su kashe kowa ba. Mun yi matukar kaduwa, mutane suka yi ta gudun tsira da ransu lokacin da suka ga 'yan bindigar dauke da AK-47 amma ba su taba kowa ba.... in ji mutumin da ya ga faruwar lamarin.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da aka janye 'yan sandan da ke bayar da tsaro a yankin da mako guda.
Sun tuntubi 'yan sanda domin jin karin bayani, amma sai suka ce za su kira daga baya.
No comments