Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Soja Da Mutum Uku A Zariya

Daga Fatima Idris Zariya A cikin daren jiya Alhamis din 27 ga watan Agustan 2021, 'yan bindiga suka sace matar wani soja da ...



Daga Fatima Idris Zariya

A cikin daren jiya Alhamis din 27 ga watan Agustan 2021, 'yan bindiga suka sace matar wani soja da mutum Uku a Unguwar Zangon Shanun Zariya dake karamar Hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Wakiliyarmu ta ziyarci Unguwar da lamarin ya faru, inda ta labarto mana cewa; 'yan bindigar sun shiga Anguwan ne da misalin karfe 11 na dare kuma suka afka gidan wani mutum mai suna Alhaji Jamilu Adamu inda yake zaune da iyalinsa kuma nan take su ka yi awon gaba da shi.

Bayanan da MADOGARA ta tattara ya tabbatar da cewa; bayan sun dauke Alhaji Jamilu sai suka fada gidan makwabcinsa inda suka taras sai matar Aure guda daya da budurwa guda daya, nan ma suka yi awon gaba da su. 

Kazalika sun yi awon gaba da matar wani matashin soja da suka riske ta da 'ya'yanta kanana guda 2, inda suka dauke ta suka bar 'ya'yan na ta kanana guda 2.

Wakiliyarmu ta ji ta bakin jama'ar yankin game da lamarin, inda wani wanda ya ce a sakaya sunansa bisa dalilan tsaro ya tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kai su 50 dauke da muggan makamai suka dira a Unguwar. 

Malamin ya kara da cewa 'yan bindigar wanda suke dauke da muggan makamai  sun ci karensu babu babbaka a wannan Unguwar.

Bincike ya nuna cewa jami'an tsaron 'yan sanda sun zo amma abin yafi karfin shirin su. 

Ya zuwa hada wannan rahoto 'yan bidiga ba su ce komai ba amma al'umma na ta tsikarin gwamnati ganin yadda kananan 'ya'yan da aka tafi masu da mahaifiya suke tsaga kuka suna neman Mahaifiyarsu .

No comments