Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 60 A Zamfara

  Hukumomi sun ce ‘yan bindiga sun sace mutane 60  a wani sabon hari da suka kai wani kauye a jihar Zamfara. Da yammacin jiya Juma’a kwamish...

 


Hukumomi sun ce ‘yan bindiga sun sace mutane 60  a wani sabon hari da suka kai wani kauye a jihar Zamfara.

Da yammacin jiya Juma’a kwamishinan yada labaran jihar, Ibrahim Dosara ya ce ‘yan bindigar sun kutsa kauyen Rini dake karamar hukumar Bakura ta jihar a daren Alhamis, inda ya ce bayan sun tafi ne al’ummar kauyen nemi mutane 60 suka rasa.

A watan ganawa da ya yi da wata tashar talabijin a kasar, kwamishinan ya ce ‘yan bindiga sun zafafa ayyukansua a jihar ne sakamakon hare-haren da sojin Najeriya ke kai musu ta sama da kasa.

Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga masu satar mutane don neman kudin fansa, inda daruruwan mutane ne aka sace ko aka kashe a cikin ‘yan shekarun nan.


No comments