Rahotanni
daga Katsina na nuni da cewa; wadansu ‘yan bindiga sun sace daliban makarantar
Islamiyya 9 a wani kauye da ke jihar Katsina mai fama da matsalar garkuwa da
mutane.
Ganau
sun tabbatar da yadda ‘yan bindigar suka shiga kauyen na Sakki haye a Babura
inda suka yi awon gaba da dalibai 8 da kuma Malami guda daya lokacin da yaran
ke kokarin komawa gida bayan tasowa daga Islamiyya.
Kakakin
rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah da ke tabbatar da faruwar lamarin ya
ce jami’ansu yanzu haka na aiki tukuru domin
ganin sun kubutar da yaran 9.
Wani
mazaunin garin Muntari Nasiru ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP
cewa da misalin karfe 6 na yammaci ne ‘yan bindigar suka shiga garin na Sakki
tare da shan gaban yaran da malaminsu guda lokacin da su ke kokarin komawa gida
bayan tashi daga Islamiyya.
Nasiru
ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun yiwa yaran da malaminsu guda barazana tare
da tilasta musu hawa kan baburan inda suka shige da su cikin daji.
Satar
mutane don neman fansa musamman dalibai a jihar ta Katsina ba sabon abu ba ne
inda ko a watan Disamban bara ‘yan bindigar suka sace wasu daliban Islamiyya
fiye da 100 a kauyen Baure gabanin nasarar ceto su daga bisani.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna
yadda ‘yan bindigar suka sace daliban da yawansu ya kai 950 daga watan Disamban
bara zuwa yanzu.
0 Comments