Tsohon gwamnan jihar Imo Chief Rochas Okorocha ya ce 'yan siyasar Nijeriya suna taka gagarumar rawa game da barakar da ke wakana tsaka...
Tsohon
gwamnan jihar Imo Chief Rochas Okorocha ya ce 'yan siyasar Nijeriya suna taka
gagarumar rawa game da barakar da ke wakana tsakanin kabilu da mabiya addini
daban-daban na kasar, lamarin dake barazana ga makomar ci gaba da hadin kan
al'umar kasar.
Okorocha
ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka.
Okorochas
na magana ne kan taron daurin auren Yusuf Buhari, da ga shugaban Nijeriya
Muhammadu Buhari da aka yi a garin Bichi na Jihar Kano a karshen makon jiya,
inda ya ce yadda manyan ‘yan siyasa suka hada kai a wurin auren ya nuna a fili
cewa, 'yan siyasar na iya magance matsalolin kasar da kansu.
No comments