'Yan Ta'adda Sun Kashe Fararen Hula 47 A Burkina FasoRfi Hausa ta labarto cewa; wadansu ‘yan ta’adda a Burkina Faso sun kashe mutane 47 cikin su harda fararen hula 30 a wani kazamin harin da suka kawai wata tawagar matafiya a yankin arewacin kasar.

Sanarwar gwamnatin kasar ta ce harin yayin sanadiyar mutuwar sojoji 14 da ‘Yan sa kai guda 3 a kusa da Gorgadji dake kasar.

Garin Gorgadji na kusurwar kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar inda aka fi samun hare haren Yan ta’adda a Yankin Sahel.

Ma’aikatar cikin gida tace sojojin da Yan sakan na gadin fararen hular take tafiya Arbinda ne lokacin da aka kai musu harin.

Sanarwar ta ce yayin musayar wutar da aka samu, jami’an tsaro sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addan 58 a fafatawar da suka yi.

Wannan hari shi ne na 3 a cikin makwanni biyu da ake kaiwa sojojin Burkina Faso abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sojoji sama da 10, tare da fararen hula 30.

Wadannan hare haren da ake samu tare da wasu rikice rikice sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,400, yayin da ya raba mutane sama da miliyan guda da dubu 300 daga muhallin su.


Post a Comment

0 Comments