YANZU-YANZU: Masu Zanga-zanga Sun Tare Hanyar Zariya Zuwa FuntuwaLabarin da ke shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa; fusatattun mutanen garin Marabar Yakawada sun tare hanyar Zariya zuwa Funtuwa, inda suke zanga-zangar Allah-wadai da gwamnati kan rashin kare rayukansu da dukiyoyinsu da ba ta yi. 


Lamarin ya auku ne da ranar yau Juma'a, inda suka tare hanyar ta hanyar kona tayoyi. Lamarin da ya jaza tsayuwar ababen hawa da za su je garuruwan Funtuwa, Zamfara da kuma Sakkwato. 

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa a 'yan kwanakin 'yan bindiga sun addabe su, inda "ko a daren jiya sun shigo sun sace mutane", inji daya daga cikin masu zanga-zangar da ya nemi a sakaya sunansa. 

Tawagar jami'an tsaron 'yan sanda sun dira a wurin masu zanga-zangar suka tarwatsa su kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana. 

Marabar Yakawada na karkashin karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna. 

Karamar hukumar Giwa na daya daga cikin kananan Hukumomin jihar Kaduna da lamarin 'yan bindiga ya ta'azzara, inda daidaikun rana ce 'yan bindiga ba sa garkuwa da jama'a domin neman kudin fansa. 

.       Ababen hawa sun yi cirko-cirko 

Post a Comment

0 Comments