YANZU-YANZU: Sojan Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Shi A Kaduna Ya Mutu


Jaridar Vanguard ta safiyar yau Laraba ta labarto cewa Sojan da aka yi garkuwa da shi da safiyar ranar Talata a makarantar horas da sojoji ta NDA dake Kaduna an tsinci gawarsa.

Jaridar ba ta yi karin bayani ba, amma ta ce Sojan mai mukamin Manjo ‘yan bindigar sun kama shi ne a harin da suka kai makarantar na NDA a Kaduna, inda suka kashe sojoji biyu nan take.

 


Post a Comment

0 Comments