YANZU-YANZU: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Kwamishinan Yada Labarai Ta Jihar Neja

 

An sace kwamishinan yada labarai ta jihar Neja, Alhaji Muhammed Sanni Idris.

MADOGARA ta labarto cewa; an sace shi ne a gidansa dake  Baban Tunga a karamar hukumar Tafa ta jihar da safiyar ranar Litinin.

Sakataren  gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da batun sace kwamishinan, inda ya ce an sace shi ne da misalin karfe 1 na dare.

Sai dai ya ce jami’an tsaro sun baza komarsu domin gano wadanda suka sace shi, inda ya bayyana kyakkwan fata na cewa za a gano inda yake tare da karbo shi cikin aminci da koshin lafiya.

 


Post a Comment

0 Comments