Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yunwa Ta Addabi Yara Fiye Da Miliyan Biyu A Arewa Maso Gabashin Nijeriya

  Daga Muhamamd A.Dalhatu MADOGARA ta labarto cewa; kungiyoyi masu ayyukan jin kai sun bayyana cewa; akalla kananan yara ciki harda ‘yan ka...

 


Daga Muhamamd A.Dalhatu

MADOGARA ta labarto cewa; kungiyoyi masu ayyukan jin kai sun bayyana cewa; akalla kananan yara ciki harda ‘yan kasa da shekaru 5 su miliyan 2 da dubu 300, suna fama da yunwa a arewa maso gabashin Nijeriya, wanda suka ce matsalolin tsaro ne ke tilastawa manoma tserewa daga gonakinsu, wanda hakan ya jefa yankin a cikin mawuyacin hali na karancin abinci.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta ‘Save the Children’ ta kiyasta cewa yanzu haka yara akalla dubu 700 'yan kasa da shekaru biyar suna cikin jimillar yara fiye da miliyan da bala’in yunwar ya shafa.

Jami'an tsaron Nijeriya dai sun shafe shekaru akalla shekaru goma suna kokarin murkushe mayakan Boko Haram da kuma reshensu mafi karfi a yanzu na ISWAP, wadanda hare-harensu cikin watannin baya -bayan nan suka halaka jami’an tsaro da fararen hula da dama, ciki har da manoma.


No comments