Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Za Mu Dauki Mataki Kan Abba Kyari - Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya

  BBC Hausa ta labarto cewa; Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta dauki matakin da ya dace kan dakataccen jami'inta Abba Kyari ...

 


BBC Hausa ta labarto cewa; Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta dauki matakin da ya dace kan dakataccen jami'inta Abba Kyari matukar aka same shi da laifin da ake zarginsa da shi.

Hukumar ta yi wannan bayani ne bayan karbar wani rahoto na musamman kan binciken da ake yi a kansa.

An mika wa Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya rahoton binciken da ake gudanar wa kan Abba Kyari, wanda aka dakatar da shi daga aiki bayan zarginsa da alaka da Hushpuppi, wanda ake kira Ramon Abbas.

Yanzu rundunar 'yan sandan ta kafa wani kwamiti da zai yi na shi binciken kan zargin da Amurka ta yi wa Abba Kyarin wanda ya musanta.

A ranar Alhamis ne Mataimakin shugaban 'yan sanda Joseph Egbunike ya mika rahoton sai dai ba a bayyana me ya kunsa ba.

Shugaban 'yan sanda Usman Baba ya yi alkawarin gudanar da binciken "ba sani ba sabo wanda za a yi a faifai".

No comments