Shugaban Amurka Joe Biden ya ce lokacin tura sojojin kasarsa kasashen ketare domin mamaya ko kuma shiga gagarumin yaki domin dawo da su ...
Shugaban Amurka Joe Biden
ya ce lokacin tura sojojin kasarsa kasashen ketare domin mamaya ko kuma shiga
gagarumin yaki domin dawo da su akan turba mai kyau ya kare.
Rfi Hausa ta labarto cewa;
Biden ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar dangane da
dalilin da ya sa ya janye sojojin Amurka daga Afghanistan, abin da ya bai wa
kungiyar Taliban damar karbe iko, Biden ya ce ba zai ci gaba da jefa rayuwar
sojojin kasar sa cikin hadari ba.
Biden wanda ya dauki
alhakin matakin da ya dauka, ya ce matakin shi ne mafi dacewa ga Amurka, duk da
korafe-korafen dake fitowa daga ciki da wajen Amurka dangane da janyewar.
Shugaban ya ce daga wannan
lokaci Amurka ba zata kwashi sojojin ta zuwa wata kasa da zimmar mamaya ko kuma
shiga yaki gadan-gadan, duk da yake kasar ba zata bada damar cutar da ita ko
muradun ta daga wata kasa ba.
Bayan shekaru 20 da mamayar
da Amurka ta yi wa Afghanistan, Biden ya ce sojojin Amurka sama da 2,400 suka
mutu, yayin da ta kashe kudin da ya kai Dala triliyan 2 da miliyan dubu 300
wajen mamayar.
No comments