Maharan dake shan luguden wuta daga Sojojin Nijeriya sun ci gaba da nausawa cikin ƙungurmin daji inda da yawan su sun shiga hann...
Maharan dake shan luguden wuta daga Sojojin Nijeriya sun ci gaba da nausawa cikin ƙungurmin daji inda da yawan su sun shiga hannu, wasu kuma tuni sun shafa lahira.
Sojojin Nijeriya ta sama da Ƙasa na ci gaba da yi wa ƴan bindiga luguden wuta a jihar Zamfara. Sun kashe da yawa daga cikin su sannan sun kama da yawa, wasu kuma sun nausa cikin daji. Sai da kuma ana bin sahun su ana kashe su.
Wasu daga cikinsu sun bi ta wasu ƙauyukan karamar hukumar Dange Shuni, sannan suka sace wasu kauyawa 20.
Kwamishinan tsaron jihar Sakkwato, Garba Moyi ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa maharan ba sace mutane suke yi ba, sukan tsorata su ne da bindigogi daga nan ko su yi sata ko kuma su barnata wuri su ci gaba da nausawa daji.
Sai dai kuma wani mazaunin kauyen Fajanbi ya shaida cewa ko a ranar Talata, Mahara sun sace mutum 9 a kauyen.
No comments