Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kashe Ɗan Muhammad Yusuf, Al-Barnawi, Jagoran ISWAP

  Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa an kashe jagoran reshen Afirka ta Yamma na kungiyar ISIS, wato ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi. Jari...

 


Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa an kashe jagoran reshen Afirka ta Yamma na kungiyar ISIS, wato ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa an kashe shi ne a karshen watan Agustan bana. Al-Barnawi dai dan Muhammad Yusuf ne, mutumin da ya kirkiri kungiyar Boko Haram.

A 2009 jami’an tsaro suka kashe mahaifinsa lokacin da kungiyar ta fara yakar hukumomin Nijeriya.

Yadda Aka Kashe Shi

Akwai ruwayoyi biyu a kan yadda aka kashe Al-Barnawi.

Wata ruwayar ta ce sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da dayar kuma ta ce ya mutu ne yayin wani fadan cikin gida a tsakanin wasu bangarori na kungiyar ta ISWAP da ba sa ga maciji da juna.

Ruwaya ta farko dai ta ta’allaka ne a kan wani bayani da wasu jami’an tsaro a bakin daga suke yadawa a tsakaninsu, wanda ke nuna cewa wani kwanton-bauna sojoji suka yi da ya kai ga kashe shi da wasu manyan kwamandojin ISWAP biyar da ma mayaka da dama wadanda suka yi masa mubaya’a.

Wata majiya ta ce an kashe shi ne a Bula Yobe, wani gari da ke kusa da iyakar jihohin Borno da Yobe a tsakanin Mobbar da Abadam.

Amma wasu majiyoyin sun shaida wa Daily Trust cewa rikicin shugabanci ne ya yi ajalin Al-Barnawi.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce rigimar ta kai kololuwa ne a tsakanin 14 da 26 ga watan Agusta, kuma rikicin ya lakume rayukan Kwamandoji da dama a bangarorin biyu.

Sai dai kuma wata majiyar ta ce daya bangaren ne ya yo hayar ’yan ta’adda daga yankin Afirka ta Tsakiya da nufin hambarar da Al-Barnawi, kuma ya yi nasara.

Tashen Al-Barnawi

A shekarar 2016 kungiyar ISIS ta sanar da nadin Al-Barnawi a matsayin jagoran reshenta na Afirka ta Yamma, Boko Haram, wadda a lokacin ke karkashin jagorancin Abubakar Shekau, wanda ya yi mubaya’a ga kungiyar ta ISIS a 2015.

Wannan lamari ne ya fito da Al-Barnawi, wanda matashi ne, sannan ya haifar da darewar kungiyar gida biyu.

An dai ce daya daga cikin dalilan da suka sa ISIS ta tsige Shekau daga jagoranci shi ne don ta ladabtar da shi bisa “saba sanannun hukunce-hukunce”, sai kuma fatan samun goyon bayan mayakan Boko Haram mabiya Muhammad Yusuf, yayin da kungiyar ke fuskantar barazana daga wasu kungiyoyin.

Shi dai Shekau ya karbi ragamar kungiyar ne bayan mutuwar Muhammad Yusuf a 2009.

-Aminiya


No comments