Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Katse Layukan Sadarwa A Wasu Sassan Jihar Kaduna

  Gwamnatin Jihar Kaduna ta soke amfani da Babura, sannan kuma ta takaita wuraren da Babura masu kafa uku za su rika shiga, domin kawo karsh...

 


Gwamnatin Jihar Kaduna ta soke amfani da Babura, sannan kuma ta takaita wuraren da Babura masu kafa uku za su rika shiga, domin kawo karshen rashin tsaro da ke neman wuce gona da iri.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka, inda ya ce matakan haramcin da zai dauki tsawon watanni uku zai fara aiki daga ranar Alhamis 30 ga watan Satunba na wannan shekarar 2021 da muke ciki. Inda aka takaita babura masu taya uku aiki daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yamma. 

Aruwan ya ce tuni gwamnatin Tarayya ta toshe layukan sadarwa a wasu yankuna jihar, bisa bukatan hukumomin Kaduna har illa masha Allahu.

Cikin matakan da gwamnatin jihar Kadunan ta dauka sun hada harda mallakar makamai.

Ya kara da cewa tuni ya aike wa gwamnatin tarayya wannan bukata wanda ya ce shugaba Buhari ya amince da matakin.

Yankunan Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kajuru da Kachia su ne suka fi fuskantar barazana daga hare-haren 'yan bindiga.

Sannan gwamnan ya ce tuni gwamanati ta kaddamar da rundunar kar-ta-kwana da za ta ke zagaye a kowanne sassa domin tabbatar da cewa mutane na bin dokokin da aka kafa domin dakile 'yan bindiga.


No comments