An Nada Fatima Waziri Shugabar NAPTIP Bayan Shugaba Buhari Ya Kori Sanata Lado


Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shugaban Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP), Sanata Basheer Mohammed.

Mohammed ya rasa kujerarsa ne watanni huÉ—u kacal da soma shugabancin hukumar.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu, ya ce Buhari ya aminta da naÉ—in Fatima Waziri-Azi a matsayin wacce za ta maye gurbin Mohammed.

Shehu ya ce naɗin Fatima ya taso ne sakamakon shawarar da Ministar Jinƙai da Agaji da Bunƙasa Zamantakewa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayar ne.

Ya ce ministar ce ta nuna buÆ™atar gaggawar da ke akwai na ma’aikatar ta ta Æ™ara himma kan Æ™arfin da hukumar NAPTIP ke da shi don cimma buÆ™atunta a muhimman wurare.

Daga nan, ya ruwaito Hajiya Sadiya na cewa an ayyana Fatima Waziri-Azi don naɗa ta a muƙamin ne duba da irin sanin makar aikin da take da shi da kuma kasancewarta mace mai hazaƙar da za ta iya tafiyar da hukumar yadda ya kamata.

Kafin wannan lokaci, Fatima ta taÉ“a yin aiki a Cibiyar Zurfafa Ilimin Shari’a ta Nijeriya kuma ‘yar gwagwarmayar yaÆ™i da cin zarafin mata, haka nan masaniyar doka ce.

Mohammed ya zama shugaban NATIP ne a ranar 27 ga Mayun 2021 inda ya gaji Misis Imaan Suleiman Ibrahim.

Post a Comment

0 Comments