An Rufe Makarantun Kwana A Adamawa Saboda Tsaro

 


Gwamnatin Adamawa ta rufe makarantun kwana 30 cikin 34 da ke fadin jihar saboda matsaloli na tsaro kamar yadda rahotanni suka labarto.

Sanarwar da kwamishiniyar Lafiya, Wilbina Jackson ta fitar na cewa an rufe makarantun daga yau Litinin har sai baba ta gani.

A cewar sanarwar an ɗauki wannan mataki bisa la'akari da taɓarɓarewa lamuran tsaro musamman kan ɗalibai a makarantu.

Adamawa na daga cikin jihohohin da ke fuskantar barazana daga hare-haren 'yan bindiga.


Post a Comment

0 Comments